A yau Litinin ‘yan majalisar dokokin jihar Legas, suka tsige kakakin majalisar, Mudashiru Obasa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin shugaban majalisar da almundahana da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Ana zargin Obasa da kashe Naira biliyan 17 wajen saka wata kofar shiga harabar majalisar.
Nan take ‘yan majalisar suka zabi mataimakiyarsa Mojisola Meranda a matsayin sabuwar kakakin majalisar.
Yanzu Mojeed Fatai ya zamo mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Legas.
Dandalin Mu Tattauna