Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi kalaman yabo ga marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, inda yayi wawaye akan yadda tsohon shugaban Amurka ya roki a sake shi a lokacin gwamnatin mulkin sojan Sani Abacha.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi yayin wani taron addu’o’in karrama Shugaba Carter wanda ya mutu yana da shekaru 100.
“Shugaba Carter na cikin abokaina na ketare da suka sadaukar da rayuwarsu domin ceton tawa tare da neman a sako ne daga kurkuku. Ziyarar da Carter ya kawo Najeriya, ta sanya Abacha amincewa ya fitar dani daga kurkuku zuwa daurin talala a gonata,” a cewar Obasanjo yayin taron addu’o’in daya gudana a majami’ar Chapel of Christ the Glorious King da ke cikin dakin karatu na Shugaba Olusegun Obasanjo, da ke birnin Abeokuta, na jihar Ogun.
“Sai dai hakan bai jima ba. Abokai da shugabannin da dama sun shiga tsakani, amma Shugaba Carter ne kadai wanda ba shugaban kasar Afirka ba, da ya ziyarci Abacha don kawai ya nemi a sake ni, kamar yadda na bada labari.”
Gwamnatin Abacha ta kama Obasanjo a 1995 a bisa zargin kitsa juyin mulki. Sai dai, an saki tsohon shugaban kasar bayan mutuwar Abacha a 1998.
Shekara guda bayan sakin nasa, Obasanjo ya zamo Shugaban Najeriya, da aka zaba karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Dandalin Mu Tattauna