Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Gurfanar Da Matar Da Aka Kama Da Damfara Ta Yanar Gizo


Internet cable
Internet cable

Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya a shiyyar Benin, tare da hada kai da abokan ta'annatin ta da ke Amurka, ta ce ta kama wata mata mai damfara ta yanar gizo.

Matar dai wacce EFCC ta kama da ke jerin mutanen da hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ke nema, ta yi amfani da hanyar musanya kudi ta yanar gizo.

Shugaban EFCC shiyyar Benin Mukhtar Bello yace an kama matar, waddda bai ambaci sunan ta ba, da take damfara ta hanyar musayar kudin BITCOIN, inda ta kan tara bayanai jagororin kamfanoni, ko kasuwanci masu hulda da ketare ta turawa 'yan uwan hadin bakin ta na Amurka, da ke aiwatar da damfarar.

Dama shugaban hukumar yaki da cin hancin Ibrahim Magu, ya bugi kirjin kama 'yan damfarar duk da sukar da hukumar ke sha na zabar wadanda ta kan yi wa dirar mikiya, da kyale wasu da ke danyen ganye, da gwamnati.

EFCC ta ce ta samu motocin alfarma a wajen matar kuma za ta gurfanar da ita a kotu a nan Najeriya bayan kammala dukkan bincike.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG