A kokarinta na karfafa tsaro a iyakokin kasashen biyu na Najeriya da Nijer dangane da fasa kwauri na miyagun kayayyaki da ake iya wuce wa dasu daga wata kasa zuwa wata kasa.
Jakadan Najeriya a jamhuriyar Nijer, Malam Aliyu Isa Sokoto shine ya jagoranci bikin mika wadannan motoci a hannun jami’an Duwan na jamhuriyar Nijar.
Malam Aliyu Isa Sokoto yace "wannan taimakon hukumar kwastan ta Najeriya ta gay a dace ta yiwa takwaranta na Nijar, saboda kamar yanda ka sani muna da iyaka da tsawonta ya kai kilomita dubu daya da dari biyar kaga yakamata a taimakawa juna domin a ci gajiyar tattalin arziki na kasashen biyu.”
A nasa bangare shugaban Duwan na kasar ta Nijer Malam Muhammadu Madu Maaiyaki ya tabbatarwa alumomin kasashen biyu aiki da wadannan motaci domin cin moriyarsu.
Wannan shine karo na farka da jami’an Najeriya ta bada taimakon wasu motoci ga jami’an tsaron gwamnatin Nijar,wanda bayar da wadannan motoci ga Nijar din na kara tabbatar da ingantatcen hurda ta kud da kud tsakanin kasashen biyu.