Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Alfanun da Najeriya Zata Samu daga Taron Tattalin Arziki


Ministar Ma'aikatan Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da shugaban bankin duniya Sakong
Ministar Ma'aikatan Kudin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da shugaban bankin duniya Sakong

Yayin da aka fara taron tattalin arziki na kasa da kasa wani masani yayi harsashen cewa babu wani alfanu da Najeriya zata samu daga taron

Najeriya zaa karbi bakuncin taron tattalin arziki na kasa da kasa to amma wani masani yana ganin babu abun da kasar zata samu.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sha buga kirji cewa taron zai jawo bimbin masu saka jari kasar domin a bunkasa tattalin arzikin kuma jama'a zasu amfana matuka. Haka ma shugaban yana ganin za'a samarma al'umma ayyukan yi sabili da taron.

To sai dai wani kwararre akan sha'anin tattalin arziki kuma malami a Jami'ar Abuja Dr Sheriff Ghali Ibrahim yace lallai Najeriya abun da zata samu daga wannan taron shi ne kudaden da wadanda zasu sauka a otel da shiga jiragen sama da cin abinci domin gwamnati zata samu haraji. Amma a zahiri bai ga wata moriya ba da kasar zata ci daga taron.

Dr Ibrahim yace muddin aka gama taron jama'a kuma suka watse sai dai Najeriya ta bisu kasashensu ta sayi kayansu. Bayan taron babu wani alfanu da Najeriya zata cigaba da samu kamar yadda kasashen waje zasu cigaba da yi.

Najeriya tana da manufa dangane da taron. Tana son yadda zata iya cigaba da bunkasa tattalin arzikinta. Tana son ta fadada kasuwanci da kasashen duniya, a kara bude hanya ta yadda kamfanonin Najeriya zasu bunkasa. Kasar tana son ta jawo hankalin kasashen duniya su saka jari a kasar. Abu mafi a'ala shi ne su kafa kamfanonin sarafa kaya a kasar maimakon a je ana sayosu daga waje.

Amma akwai matsala domin kwanakin baya ana kama turawa ana garkuwa dasu. Shin wane bature ne zai yadda ya zo ya kafa ma'aikata a Najeriya yanzu. Babu tsaro. Idan kuma ba'a inganta tsaro ba ba za'a samu cigaba ba musamman a fannin tattalin arziki. Rashin isasshiyar wutar lantarki shi ma matsala ne. Akwai kuma lalaci ta hanyar kudi da aka san 'yan Najeriya da shi. Cin hanci da rashawa sun yiwa kasar katutu. Kasashen waje da zasu zo suna kokari su yaki cin hanci da rashawa a koina domin a tsaftace duk kudin da zasu shigo ko kuma za'a kashe. A Najeriya wadanda suke ikirarin yin yaki da cin hanci da rashawa su ne suke karbar cin hancin.

Ga karin bayani.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG