Rundunar ‘yan Sandan jihar Legas, ta cafke wata mata mai matsakaicin shekaru mai suna Linda Alapa, wanda ake zargi da dukan wata yariya Joy Mbafan, mai shekaru goma da haihuwa mai zaman ‘yar aikinta har lahira.
Jaridar Punch, ta ruwaito cewa misalin karfe ukku na dari Alapa, ta fara dukan yarinya saboda tayi laifi dukkan da daga bisani yayi sandiyar mutuwarta.
Bayan da yarinyar ta mutu sai ta dauki gawar ta kai asibiti, inda Likitan dake aiki ya ga shedar azabtarwa a jikin gawar sai ya sanarda ‘yan Sanda, wadanda su kuwa basu yi kasa a guiwa ba suka damke ta.
Wata majiyar ‘yan Sanda, tace a lokacin da ake yimata tambayoyi, Linda Alapa, ta amsa cewa ta doketa majiyar ta kara da cewa za’a tuhumeta da laifin kisan kai.
Wasu makwabta da aka zantadasu sun ce sun dade suna jamata kunnen akan azabtar da yarinyar da take yi.
Kakakin 'yan Sandan jihar Legasm SP Dolapo Badmos, wace ta bada tabbacin afkuwar lamarin tace za'a gudanar da bincike akan gawar ita kuma matar zata gurfana a gaban kuliya.