Bayanai dai daga yankin sun nuna cewa 'yanfashin dajin basu samu nasarar kama daliban ba, to amma sun hallaka daya daga cikinsu a lokacin da yake kokarin tserewa daga makarantar.
Wani mazaunin yankin da ya tsallake rijiya da baya kuma ya nemi a sakaya sunansa yace ya zuwa lokacin da muke magana dashi suna cikin wani yanayi na tashin hankali.'
Kawowa lokacin hada wannan rahoto babu wani karin haske daga gwamantin jihar Nejan akan wannan sabon harin domin kokarin samun sakataran gwamnatin jihar ta wayar salula yaci tura.
Shugaban riko na karamar Hukumar Mariga Hon. Abbas Adamu Kasuwar Garba ya tabbatar da kashe wannan dalibi da a ka ce ya je makarantar ne domin rubuta jarabawar NECO.
Rundunar yansandan jihar Nejan ma ta tabbatar da kai wannan hari. A hirar shi da Muryar Amurka, kwamishinan 'yan sandan jihar Monday Bala Kuryas yace suna gudanar da bincike akan lamarin domin basu tabbatar da abinda ya faru a wurin ba.
Yanzu haka dai bayanai sun nuna cewa akwai garuruwa da dama a wasu yankuna na kananan hukumomin jihar Nejan da mutane su ka kauracewa a sakamakon wannan matsala ta 'yan fashin daji masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti :