Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Korea ta Arewa Da Taimaka wa Assad Wajen Hada Makamai


Wani rahoto ya zargi Korea ta Arewa da taimka wa kasar Syria wajen hada makamai masu guba da ake zargin tana amfani da su wajen kai hari kan 'yan tawaye.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya na nuna cewa Korea ta arewa ta kai wasu kayayyaki a Syria da ta yi wu gwamnatin Bashar al-Assad ta yi amfani da su wajen yin makamai masu guba.

Rahoton ya ce wasu abubuwa kamar na'urar auna yanayi da sauransu na cikin akalla kayayyaki 40 da ba a ba da rahotonsu ba da Korea ta arewa ta kai Syria a tsakanin 2012 da 2017.

An ba wasu kafafen yada labarai wannan rahoton a daidai lokacin da Amurka da wasu kasashe ke zargin gwamnatin ta Syria da yin amfani da makaman guba akan farar hula.

An ga kwararru a fannin kimiyar makamai masu linzami na Korea ta Arewa na aiki a wuraren kera makamai masu guba da masu linzami na Syria, a cewar rahoton, wanda wasu kwararru da suka yi binciken kwakwaf akan yadda Korea ke kiyaye takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG