Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Ya Rufe Taron Farfado Da Tafkin Chadi A Abuja


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari
Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya ya halarci taron farfado da tafkin Chadi da aka kwashe kwanaki hudu ana yi inda ya jaddadawa takwarorinsa da sauran masu ruwa da tsaki cewa wajibi ne a yi jaddawalin aikin farfado da tafkin ba wai a watse daga taron ba a kuma jira sai wata shekarar

Shugaban Najeriya ya jagoranci sauran kasashen dake kewayen tafkin chadi a taron farfado da tafkin da ya kawo karshe a Abuja.

Shugaban Najeriya ya bukaci a tabbatar a wannan karon za'a shirya tsarin farfado da tafkin dalla dalla ba maganar ta sha ruwa ba bayan an kammala taron. Ya jaddada mahimmancin tafkin wanda kasashen Afirka ta yamma da ta Afirka ta Tsakiya suka dade su cin gajiyarsa.

Ya tuna masu yadda bushewar tafkin ya kawo matsaloli na zamantakewa da sufuri da ayyukan bunkasa tattalin arzikin yankin, musamman noma da cinikayya.

Shugaban Najeriya ya kira sauran takwarorinsa da kungiyoyi da babban bankin duniya da bankin Islama da kungiyoyin dake kula da rayuwar al'umma su himmatu wurin tabbatar da cewa an dauki matakan da suka kamata domin farfado da tafkin.

A cewar shugaban a karshen taron za'a fitar da matsayi na Abuja akan taron, wato za'a fitar da wata tausiya ce za'a yi anfani da ita wajen shirya jaddawalin aikin gyara tafkin dalla dalla. Ya ce duk masu ruwa da tsaki su amince da kudurin su tashi su yi aiki tukuru ba wai su mayar da taron wani taron shan shayi ba.

A saurari rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:42 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG