Da farko dai kotun sojin ta caji sojojin da laifin cin amannar kasa, inda ta yanke musu hukuncin kisa.
To amma daga baya an yi bitar hukuncin, aka kuma mayar da shi zaman kurkuku na tsawon shekara 10, aka kuma tsare su a gidan gyaran hali na Kirikiri da ke Apapa, a birnin Legas.
An saki sojojin ne yayin da ‘yan uwa da iayalansu suka tarbe su a farfajiyar gidan yarin, kana daga bisani suka shiga mota zuwa ofishin Femi Falana.
Falana wanda shi ne ya tsaya musu a zaman shari’ar da aka yi musu, ya ce “zargin aikata laifi daya ne kacal aka sami tabbatarwa a kan su a kotun ta soji, wato yin zanga-zanga akan kasawar hukumomin soji na samar musu isassun makamai domin yaki da ‘yan ta da kayar baya.”
Falana ya ci gaba da cewa “ba kamar wasu sojoji da dama da suka gudu daga aikin na soji ba, wadanda aka yanke wa hukuncin sun zabi tsayawa domin kare martabar kasa. Abin da kawai suka yi shi ne meman kayan aikin yaki da ‘yan ta’adda wanda kuma halataccen abu ne.”
Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar ThisDay cewa za’a dauki sojojin da aka sako zuwa shelkwatar tsaro a Abuja domin ganawa da babban hafsan tsaro da hafsan sojin kasa.
Haka kuma an tsara gudanar da wani shirin daidaita hali da kwakwalwa ga sojojin da aka sako a Eket na jihar Akwa Ibom, domin kimtsa su da saukaka komawarsu a cikin al’umma.