Magajin garin Kamfala na kasar Uganda da aka sake zaba a zaben kasar na watan Fabrairun da ya gabata Erias Lukwago yace, ba zai yiu kasa a gwuiwa ba game shiga ofishinsa na mulki ba.
Duk kuwa da cewa jami’an kasar sun hana tawagarsa shiga ofishin nasa gabanin fara aikinsa. Mista Erias ya zargi shugaban kasar Yoweri Museveni da gaza fahimtar karfin bukatar mutanen kasar game da yiwuwar sake zabarsa a ranar 18 ga Fabrairun bana.
Hukumar zaben kasar ce dai ta sanar da nasarar Lukwago da kaso 82 na kuri’un da aka kada, inda ya doke abokin hamayyarsa Daniel Kazibwe na jam’iyyar NRM, wanda ya sami kaso 20 kacal daga yawan kuri’un.
An dai tsige Erias ne daga mukaminsa a bayan lokacin da mahukunta suka zarge shi da cin mutuncin kujerarsa da kuma rashin da’a da rashin cancanta. Daga baya kuma wata kotu da a baya ta yarda da tsige shi ta dawo ta ce tsige shin ya sabawa doka.