An Sake nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a wani sabon wa’adin shekaru hudu.
Wa’adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2025 kamar yadda shafin shafin yanar gizon WTO ya wallafa a ranar Juma’a.
“Matakin ya nuna cikakken amincewa da jagorancin ta na musamman da hangen nesan ta na ci gaban WTO nan gaba.” A cewar shafin na WTO.
An fara aikin sake nadin nata tun a ranar 8 ga Oktoba, 2024, wanda Jakada Petter Ølberg daga kasar Norway, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, ya jagoranta.
“Tunda babu wani karin dan takara da aka gabatar kafin wa'adin ranar 8 ga Nuwamba ya cika, Dr. Okonjo-Iweala ita ce kaɗai ta tsaya takara.” A cewa Majalisar Kolin kungiyar ta WTO.
An gudanar da wannan mataki cikin tsari da gaskiya, daidai da dokokin WTO kan "Tsare-tsaren Nadin Daraktoci Janar mai lamba (WT/L/509).”
Dr. Okonjo-Iweala wacce ‘yar asalin Najeriya ce, ta fara wa’adinta na farko a ranar 1 ga watan Maris 2021. Ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami
Dandalin Mu Tattauna