Hukumar kasuwanci ta duniya (WTO) ta bayyana cewar za ta gudanar da taron majalisar zartarwarta na musamman domin fadada tsarin zaben shugabanta mai zuwa.
Sanarwar da shugaban majalisar zartarwar, Jakada Petter Olberg dan kasar Norway ya fitar a jiya Talata, tace taron zai gudana ne a tsakanin ranakun 28 da 29 ga watan Nuwamban da muke ciki.
Taron ya biyo bayan sanarwar da shugaban majalisar zartarwar ya bayar a ranar 9 ga watan Nuwamban da muke ciki ta cewa har zuwa cikar wa’adin 8 ga watan Nuwambar da aka tsayar domin mika sunaye, babu dan takarar da ya fito domin neman mukamin, in banda shugabar dake kan kujerar a halin yanzu, Ngozi Okonjo-Iweala.
A sakon da ya aikewa mambobin majalisar, Jakada Olberg yace, a bisa ganawar da ya yi da wakilai a ‘yan kwanakin da suka gabata, kuma kamar yadda ta kasance a baya inda shugabar dake kan kujerar ce kadai ‘yar takara, yana da niyar kiran taron musaman na majalisar zartarwar tsakanin ranakun 28 da 29 ga watan nuwambar da muke ciki.
Dandalin Mu Tattauna