An sako babban dan marigayi shugaba Muammar Gaddafi na kasar Libya, kuma wanda aka zaci zai gaji mahaifinsa a mulki, Seif al-Islam Gaddafi, a bayan da aka shafe shekaru fiye da 5 ana tsare da shi, a cewar wadanda suka tsare shi.
Wata sanarwar da Bataliyar Abubakar Al-Siddiq wadda ta rike Seif al-Islam ta bayar, ta ce an sake shi shekaranjiya Jumma’a, amma ba ta bayarda Karin haske kan inda yake ba. Wasu jami’an Bataliyar da kamfanin dillancin labaran AP ya tuntuba a cibiyarsu a garin Zintan dake kudu da Tripoli, sun gaskata rahoton sake shi. Amma sun ki su bayyana inda yake a saboda abinda suka bayyana a zaman damuwa kan tsaron lafiyarsa.
Suka ce an sake shi ne a karkashin wata ahuwar da majalisar dokokin Libya mai cibiya a gabashin kasar ta bayar kwanakin baya.
Majalisar dokokin dake birnin Tobruk, tana biyayya ga daya daga cikin gwamnatoci guda uku da ake da su a kasar Libya yanzu haka, shaida ta irin wargajewar al’amura da Libya ta samu kanta ciki tun bayan da aka hambare Gaddafi aka kashe shi.
Mayakan bataliyar sun kama dan na Gaddafi a karshen shekarar 2011, shekarar da aka hambarar da mahaifinsa daga kan mulki aka kuma kashe shi.
Facebook Forum