Yanzu haka dai jami'an tsaro a jihar Taraba sun bazama wajen gano inda aka sulale da wadannan matafiya da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da jama'a ne suka yi awon gaba da su.
“Bayanan da muke da su, su ne, mutanen sun fito ne daga biki na aure, daga baya sai aka samu motarsu ba kowa, ba a san mene ne ya faru da su ba.” In ji DSP David Misal, Kakaki a rundunan ‘yan sandan jihar Tarabar.
Wannan lamari dai ya ta da hankulan jama'a, musamman kungiyoyin kare hakkin dan Adam.
Kuma wannan na zuwa ne yayin da jama'a ke nuna alhini na garkuwa da kuma kisan da aka yi wa Shugaban karamar hukumar Ardo Kola.
Kawo yanzu dai tuni jami'an tsaro suka ba zama don ceto wadanda aka yi awon gaba da sun.
Najeriya dai ta jima tana fama da matsalar masu garkuwa da mutane don neman kudion fansa, musamman ma a arewacin kasar, lamarin da ya zama babban kalubal ga hukumomi.
Ga karin bayani daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz: