Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta kuma bayyana cewa maharan sun cinna wa gawarwakin jami’an da motocinsu wuta.
“Gwamnatin jihar Anambra ta yi bakin cikin aukuwar wannan al’amari mai ban takaici, wanda ke zuwa a lokacin da jihar ta fara ganin ci gaba a fannin tsaro," a cewar Mr. Christian Aburime, kakakin gwamnatin jihar.
Gwamnatin jihar ta kuma yi Allah wadai da wannan harin kuma ta sha alwashin zakulo duk wadanda suka aikata wannan ta’asar a duk inda suka boye.”
Ya zuwa yanzu dai ba a kama maharan ba, amma ‘yan sanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike da farautarsu a karamar hukumar Ogbaru inda harin ya auku.
“Aiki na ci gaba da gudana. An kaddamar da bincike a garin Ogbaru,” a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga. Ya kuma ce zasu bada karin bayani nan gaba.
Tuni dai Fadar White House ta Amurka ta bayyana cewa ma’aikatan ofishin jakadancin nata ‘yan Najeriya ne harin ya rutsa da su, amma babu wani Ba’amurke a cikinsu.
Karamar hukumar Ogbaru na kara kaurin suna a jihar Anambra da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, don ko a watan Afrilun bara wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda a garin Atani da ke karamar hukumar, inda suka hallaka ma’aikata hudu.
Saurari rahoton cikin sauti: