Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Fitaccen Mawakin Siyasa Alhaji Ado Daukaka


Ado Daukaka
Ado Daukaka

Rahotanni daga jihar Adamawa Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sun sace wani fitattacen mawakin siyasa biyo bayan sake wata sabuwar waka da ya fitar mai suna Gyara Kayanka, inda ya caccaki wasu kusoshin siyasar jihar game da batun wakaci-ka-tashi da ake zargin ana yi da dukiyar jihar.

Alhaji Ado Daukaka yayi fice wajen fayyace gaskiya komi dacinta, tuni kuma kungiyoyi suka soma yin Allah Wadai da kiran a sako shi.

Kuma tun ranar asabar ba’a san inda aka yi da shi ba.

Iyalan mawakin wanda ke cikin zulumi da damuwa sunce an sace shi ne, da sanyin safiya, bayan ya taso daga massalacin anguwarsu yana komawa gida wanda kuma kawo yanzu ba a san inda aka yi da shi ba, domin an bincika wajen jami’an tsaro amma babu bayani.

Wannan shine karo na biyu da aka sace mawakin siyasa, bayan da aka sace fitattacen mawakin nan, Rara wanda kamar yadda rahotanni suka tabbatar sai da aka bada kudin fansa kafin a sako shi.

Awon gaban da aka yi da Ado Daukaka, yanzu haka ya tayar da hankulan jama’a inda kungiyoyin fafutuka a jihar ke ganin da walakin.

Hon Hussaini Gambo Bello, dake zama shugaban hadakar kungiyar cigaban jihar Adamawa ta Adamawa Concern Citizen, yace gargadi wadanda suka yi awon gaba da mawakin da suji tsoron Allah.

Shima wani na kusa da mawakin kuma dan fafutuka a jihar ,Comrade Atiku Mustapha Ribadu, ya bayyana halin da iyalan mawakin ke ciki a yanzu inda yace tun ranar asabar basu san inda aka yi da Ado Daukaka ba.

To sai dai kuma, kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawan,SP Othman Abubakar wanda yace, a hukumance bai da cikakken bayani, to amma kuma ba zasu kyale ba, ganin cewa jihar ta yi fama da matsalar satar mutane, domin neman kudin fansa ko da yake an fara samun sauki a yanzu.

Kawo yanzu dai tuni aka soma gangami ta dandalin sada zumunta na neman a ceto mawakin Ado Daukaka, yayin da wakar ‘’Gyara Kayanka’’ ke zama abun cecekuce.

XS
SM
MD
LG