Babban hadarin hunturun ya zo dauke da dusar kankara da kankarar da iska tare da sabbaba sanyi mai tsanani a fadin Amurka da kuma kawo cikas ga harkokin sufuri tun daga jihohin tsakiya zuwa na kudanci ya zarce zuwa gabar tekun dake gabashin kasar a yau Litinin, abin da ya tilasta makarantu da ofisoshin gwamnati rufewa a jihohi da dama.
Dusar kankara da kankara sun lullube manyan hanyoyi a fadin jihar Kansas da yammacin Nebraska da wani yanki na Indiana, inda aka umarci rundunar askarawan tsaron kasar su taimaka wa masu ababen hawan da suka makale.
Ana sa ran samun dusar kankarar da akalla tudunta ya kai sentimita 20, tare da iska mai karfi mai gudun kilomita 72 cikin sa’a guda.
Hukumar kula da yanayin kasar ta fitar da gargadi a kan hunturu daga jihar Kansas zuwa Missouri ya zarce zuwa New Jersey.
“Ga jihohin dake wannan yankin da suka samu adadin dusar kankara mai yawa, hakan na iya zama zubar dusar kankara mafi karfi da aka gani cikin gomman shekaru,” a cewar hukumar kula da yanayi ta Amurka.
Dandalin Mu Tattauna