A ranar litinin ne jami’an agajin gaggawa da na masu kashe gobara na karamar hukumar Accokeek, a jihar Maryland. Suka ceto ran wata mata da ta makale a cikin motar ta, har na tsawon kwanaki uku, biyo bayan mahaukaciyar dusar kankara da akayi a jihohin yankin Arewa maso gabashin kasar Amurka.
Ita dai wannan matar tana cikin motar ta lokacin da wannan dusar kankarar ta fara sauka, tana tunanin bari ta tsaya idan ta rage sai ta fita ta shiga gida, daga baya dusar kankarar ta rufe motar ba’a ko ganin motar. Tun ranar juma’a take cikin motar har zuwa litinin ba a gane ba, sai da makocin ta yayi ta kokarin kiranta a waya amma baya samun ta.
Daga nan sai ya sanar ma hukumomi, kodai da aka samu aka fitar da motar daga cikin kankara sai aka same ta cikin wani hali, daga nan dai an garzaya da ita asibiti don duba lafiayr ta.