Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Shugaban Majalisar Dattawan Haiti A Birnin Port-au-Prince


 Shugaban majalisar dattawan kasar Haiti Joseph Lambert
Shugaban majalisar dattawan kasar Haiti Joseph Lambert

Wasu ‘yan bindiga ne suka harbi shugaban majalisar dattawan Haiti Joseph Lambert a ranar Lahadi a wata unguwa da ke kusa da ginin majalisar dokokin kasar a birnin Port-au-Prince.

Wani dan uwan shugaban majalisar ya shaida wa Muryar Amurka cewa ana yi wa Lambert jinya a wani asibiti da ke babban birnin kasar saboda raunin da ya samu.
Lamarin dai ya faru ne kwanaki biyu gabanin cikar wa’adin wasu ‘yan majalisar dattawa, wadanda a yanzu haka sune kadai zababbun ‘yan siyasa a Haiti.

Kasar Haiti dai na kokarin shawo kan yawaitar tashe-tashen hankulan kungiyoyin bata gari da satar mutane, lamarin da ya sa gwamnatin kasar a watan da ya gabata ta yi kira ga kasashen duniya da su taimaka mata.

Gwamnatin Firai Minista Ariel Henry na neman agaji cikin sauri a Haiti domin taimakawa wajen kawar da tashe tashen hankulan kungiyoyin miyagu.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tattauna game da batun, amma bai yanke shawara ba.

Ariel Henry
Ariel Henry

Lambert na daya daga cikin 'yan siyasar Haiti biyu da Baitulmalil Amurka ya sanya wa takunkumi a cikin watan Nuwamban 2022. Jami’an Amurka sun zargi Lambert da hannu a harkar safarar miyagun kwayoyi.

Haka ita ma kasar Canada ta sanya wa dan siyasar takunkumi.

Santa Lambert dai ya musanta zargin kuma ya sha alwashin kalubalantar takunkumin a kotu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG