Murabus din na Henry na zuwa ne bayan da shugabannin yankin suka gana da safiyar jiya Jamaica da ke kusa da kasar, domin tattaunawa kan tsarin mika mulki, wanda Amurka ta kira a makon da ya gabata da a “gaggauta” tare da kafa Majalisar Shugaban kasa yayin da gungun bata gari suka yi kira ga Henry ya yi murabus.
Henry ya tafi Kenya ne a karshen watan da ya gabata domin tabbatar da jagorancin tawagar tsaro ta kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ke marawa baya don taimakawa ‘yan sanda yaki da ‘yan fashi da makami, sai dai wani mummunan tashin hankali da ya barke a babban birnin Port-au-Prince a lokacin da ba ya nan ya yi sanadiyar makalewarsa a yankin Puerto Rico.
Dandalin Mu Tattauna