A janhuriyar Nijer yan majalisun dokokin kasar sun zabi Honorable AMADOU SALIFOU a matsayin sabon kakakin majalisar dokokin kasar.
'Yan adawar kasar dai sun kauracewa zaben inda sukayi zargin cewar an ajiye takarar ta sabon kakakin ba tare da bin ka'ida ba.
Sabon kakakin zai maye gurbin tsofon kakakin majalisar kasar Malam HAMA AMADOU da kotu ta zarga da safarar jarirai kuma yake gudun hijira a kasashen waje tare da cewar ana son a yi masa bita da kulli ne kawai irin ta siyasa.
A makon jiya ne kotun kolin kasar tace kujerar ta shi Hama Amadou ta kasance kanguwa saboda hakan a gaggauce ‘yan majalisar su zabi wani sabon kakaki ga majalisar a cikin wa'adin kwanakki 15.
Nan da ‘yan kwanaki kalilan ne ake shirin rantsar da sabon kakakin majalisar wanda masu manazartar siyasa suke gani yana da jan aiki a gabansa, ganin irin halin da majalisar dokokin janhuriyar Nijar take ciki, mai nasaba da rudani da kasar take fuskanta.