Babban sakataren kungiyar a Najeriya Alkassim Yahaya, ya ce haka kawai sojojin Burkina Faso suka tsayar da jerin gwanon motocin 'yan darikar suka zabi wadanda suke so suka yi musu kisan gilla.
Kungiyar ta Ansaru ta bukaci majalisar dinkin duniya, da kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta yamma ta ECOWAS, da sauran gwamnatoci su duba wannan kisan gilla don bin kadin wadanda aka kashe ba gaira ba dalili.
Yahaya ya ce zasu mika takardar korafi ga duk sassan da suka dace don hukunta wadanda suka yi kisan da kuma biyan diyya ga iyalan marigayan.
Kungiyar ta ce hakan bai taba aukuwa ba a baya, don Tijjanawa kan shiga mota da takardunsu na shaidar tafiya su kai ziyara Kaulaha a Senegal ba tare da samun cikas ba.
Muryar Amurka ta tuntubi karamin Minista a ma'aikatar harkokin wajen Najeriya Ambasada Zubairu Dada, ya ce tabbas za su bi kadin marigayan.
A halin yanzu, sauran ‘yan tawagar da suka tsallake rijiya da baya sun samu damar ci gaba da tafiyarsu don isa Senegal cikin yanayin juyayin abin da ya faru.
Saurari rahoton cikin sauti: