Sanusi Ajiya yace kasashen duniya da suka ci gaba na tattare da shuwagabani masu aiki tukuru domin ganin 'yan kasuwa sun sami kyakyawan yanayi domin bunkasar kasuwanci.
A cewarshi, babu ruwan gwamnati da kasuwanci, amma dokokin da take yi akan harkokin kasuwanci wajibi ne ta ringa tuntubar 'yan kasuwa domin samun ra'ayoyinsu dangane da haka.
A wani labari kuma tsohon dan majalisar wakilai,mai wakiltar mazabar Katagum ya gwamnati,sai dai ta taimaka da bukatun 'yan kasuwa da yakamata akan harkokin kasuwa domin kasuwanci ya tsaya dai-dai.
Ya kara da cewa dogaro da gwamnati bana dan kasuwa bane.