'Ya'yan kungiyoyin sun hada da tsoffin malaman makaranta da tsoffin ma'aikatan gwamnati mata.
Matan sun yi koken ne a wani taron manema labarai da suka kirawo a birnin Miduguri fadar gwamnatin Borno.
A wurin taron manema labarai, matan sun nuna rashin jin dadinsu da kalamun batanci da suka ce wasu bangarorin kasar na yiwa arewa da al'ummarta.
A jawabin da ta yi Dr Aisha Yusuf Gombe, ta ce an nunawa arewa kiyayya musamman a siyarsa bana ta kara da cewa an gama zaginsu kakaf.
Tace maganar 'yan Chibok ma an mayar dasu banza. Maimakon su tausaya mana sai suka yi watsi damu-inji Aisha. Sun mayar da harakar abun siyasa. Duk fitinun da aka samu a arewa sun mayar dasu siyasa.
Dr Aisha tayi misali da matar shugaban kasa. Tace wacce ta kamata ta zama itace uwar kowa tunda mijinta shi ne uba sai ta nuna cewa ita uwar mutanen 'yan kudu maso kudu ne da kudu maso arewa.
Duk lokacin da mata ke cikin wahala a arewa ko sau daya matar shugaban kasa bata leko ba. Amma duk wasu kayan tallafi mutanensu take kaiwa har ma kasashen waje take kaiwa kamar Kamaru, Kotonu da sauransu. Ta kai masu abinci da kayan sawa.
Matar shugaban kasa ta fada cewa 'yan arewa ba mutane ba ne. Tace mutanen arewa na haifan yara suna jefar dasu a tituna. Dr Aisha tace abubuwan da matar shugaban kasa ta fada game da arewa sun yi yawa bai kamata ma a sake maimaitasu ba.
Dr Aisha ta cigaba da cewa irin su Fanikayode da Fayose da Edwin Clark suna son su kawowa kasar rudani ne kawai wajen daurawa Janar Buhar karan tsana. Tace babu abun da Fanikayode ya sa a gaba saidai zagi da sharrin da yake yiwa Janar Buhari.. Baya iya zama bai zagi Janar Buhari ba. Edwin Clark, tsohon da ya kamata ya koyawa yara zaman lafiya da tsare gaskiya ya zama tsohon najadu.
Man da suke ikirarin nasu ne da kudin gyada da auduga daga arewa da kudin kokon Yarbawa aka hakoshi. Dr Aisha tace Fanikayode, Clark, Fayose da Dokubo sun hada rikici tsakanin Jonathan da mutanen kasar da dama.
Ga karin bayani.