Wakiliyar muryar Amurka Madina Dauda, dake birnin tarayya Abuja, na daya daga cikin matan da suka halarci wannan taron a karkashin wata kungiya mai zaman kanta da ta wakilta.
A wata hira da muryar Amurka, Madina tace an yi bitar ne don sake waiwayar taron da aka yi a Beijing, shekaru 20 da suka wuce don duba cigaban da aka samu ko ake samu game da kaso 30 cikin dari na mukaman da ya kamata ace mata sun samu a kashen duniya, musamman kasashe masu tasowa, da kuma kalubalen da mata ke fuskanta.
Duk da cewa ba a basu damar yin jawabi a babban dakin taron ba, Madina ta ce suna sa ran nan gaba za a yi hakan.
“A wannan taron kasashe da yawa sun gabatar da takardu na damuwa da kokensu akan yadda ake tafiyar da harkokin mata a kasashen su”, inji wakiliyar ta Muryar Amurka.
“An sami cigaba wajen nada mata mukamai a Najeriya cikin ‘yan shekarun nan, a karkashin gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan fiye da yadda aka samu a gwamnatocin baya. Amma a fagen siyasa kuma har yanzu dai kwalliya bata biya kudin sabulu ba, a ta bakin Madina.
Wakiliyar ta Muryar Amurka ta kuma ce, ya kamata a ce a cikin jihohi talatin da shida na Najeriya, akwai mata sama da kashi talatin da biyar cikin dari rike da mukamai, amma ko kashi 20 ba a samu ba a majalisar tarayya yanzu haka. Ta kuma ce kamata yayi mata su fito su taka rawa a zabe su don samun mukaman siyasa, kamar yadda suke goyon bayan maza.