Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Garbai Umar Ibn El-Kenemi, yayi kira ga 'yan Najeriya su guji tarzoma da duk wani al'amari da zai jawo tashi hankali kamin a fara zabe, lokacin da ake gudanar a zaben da kuma bayan zabe.
Alhaji Abubakar wanda yayi wannan kiran lokacinda yake karbar katin zabensa na din-din-din, a wani biki da aka yi a fadarsa domin haka, yace musamman matasa da kuma 'yan siyasa su guji duk wani abu da zai jawo tashin hankali ko tarzoma tsakanin al'uma.
Shehun na Barno yace, a makon jiya ma sai da duka manyan sarakunan gargajiya daga jihohin arewan nan 19 suka yi wani taro a kaduna kan batun neman a tabbatar zaman lafiya. Ya kara da cewa zasu ci gaba da ilmantarda al'umominsu kan muhimmancin zaman lafiya.
Yayinda Shehun Barno yake karbar katin zabensa wasu mazauna birnin na Maiduguri sun koka kan rashin karbar katunan zabensu. Wasu daga cikinsu sun gayawa wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda cewa, sun yanke shawarar yin zaman dirshen a harabar hukumar zabe har sai an basu katunan zabensu.
Amma da yake magana, kwamishinan hukumar zaben a jihar Samuel Usman Madaki, ya roki jama'a su kara hakuri domin a cewarsa yanzu haka motoci daga Abuja sun doshi jihar dauke da katunan zaben, kuma ma'aikatansa zasu yi aiki ba dare ba rana, wajen ganin kowa ya sami katinsa.
Ga karin bayani.