Shugaban Kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Bello Badejo ya shaida wa Muryar Amurka cewa har yanzu basu ji komai ba daga bangaren gwamnatin Najeriya, musamman game da abunda ya shafi diyya, ko kuma wani tallafi ga iyalan wadanda akayi wa kisan gillar.
“Akwai wadanda suka taimaka wa iyalan wadannan wadanda sojoji suka kashe. Babu abinda gwamnati ta bayar game da wannan al-amuran,” a cewar Alhaji Abdullahi.
Mr. Badejo ya bayyana takaicinsa ga yadda gwamnati taki fitowa domin bada hakuri game da abunda ya faru.
“Ya kamata ta fito ta gayawa duniya cewa ayi hakuri. WalLahi ko jaje ba’a yi mana ba, babu komai,” inji Alhajii Badejo.
A halin da ake ciki dai, shugabannin al-ummar Fulanin sunce sun damu matuka akan halin kunci da sukace Fulanin na ciki.
A yanzu dai shugabannin Fulanin sunce sun dukufa wajen wayar da kan makiyaya musamman gameda neman ilimin da zai taimaka wajen cigaban rayuwarsu.