Za’a dage shirin da akan yi a gabatarda babban jawabin shekara-shekara na “halin da kasa ke ciki” da ya kamata shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya gabatar jibi Alhamis, abinda ke kara tsananta matsin lambar da ake yiwa shugaban na ya sauka daga karagarsa ta mulki.
Shugabar majalisar dokoki Baleka Mbete ce ta bada sanarwar jingine gabatarda jawabin yayinda take hira da manema labarai yau a birnin Cape Town, inda ta bada hujjar cewa “ana neman samarda yanayin masalaha na siyasa a cikin majalisar” kafin a yi jawabin.
An dai jima ana matsawa shugaba Zuma lambar yayi murabus tun bayanda aka sauke shi daga kujerar shugabancin jam’iyya mai mulki ta ANC a watan Disamban da ya gabata a sanadin zargin cin hanci da rashawa da ake mishi.
An kuma zabi tsohon mataimakinsa, Cyril Ramaphosa don ya maye gurbinsa a shugabancin na ANC.
Facebook Forum