An kashe daya daga cikin manyan masu binciken haramtaccen cinikin hauren giwa da na karkanda a fadin duniya.
Jiya Lahadi ne aka sami Esmond Bradley Martin, a mace a gidansa, da alamun an daba masa wuka a wuyansa, a gidansa dake birnin Nairobin Kenya.
An san Esmond, haifaffean Amurka mai shekaru 75 da aiki cikin sirri wanda yake kai ga bankado asirin masu fasakkaurin hauren giwa da kuma masu saya.
Shugabar ma'aikatar kungiyar da take kare muradun dabbobi, Paula Kahumbu tace binciken da Martins yayi ya taimaka wajen tona asirin masu cinikin hauren giwa da karkanda dake Amurka, da Congo, da Vietnam, da Nigeria, da Angola, da China, da kuma Myanmar a baya bayan nan. Aikin shi ne ya tilastawa China, ta hana cinikin Hauren giwa ta haramtacciyar hanya a shekarar 1993.
Binciken da marigayin ya yi shine kuma ya taimaka wajen kawo cinikin hauren giwa ta hanyoyin halal a China, dokar da ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Junairun bana.
Facebook Forum