Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Babban Hafsan Soja A Somalia


.
.

An kashe wani babban hafsan sojin Somalia a wani harin bam na cikin mota a Mogadishu, babban birnin kasar a jiya Lahadi.

Janal Mohammed Roble Jimale mai lakabi Goobale da wasu dogarawansa guda shida ne suka mutu acikin jerin motocinsu, yayid da wata mota dauke da dimbin bama-bammai ta abka musu kusa da kofar shiga helkwatan ma’aikatar tsaron Somalia a can Mogadishu, a cewar Abdifitah Omar Halane, kakakin hukumar birnin Mogadishu a hirarshi da Muryar Amurka.

Tuni kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin.

Koda yake tun shekarar 2011 Rundunar sojan kiyaye sulhu ta kungiyar Taryyar Kasashen Afrika ta fitar da mayakan al-Shabab daga birnin Mogadishu, har iyau al-Shebab na ci gaba da gallazawa mazaunan birnin na Mogadishu, ta hanyar kai hare hare da zummar hambarar da gwamnatin kasar mai samun goyon bayan kasashen yammacin duniya.

XS
SM
MD
LG