Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Tara A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya


Akalla mutane 20 aka hallaka a kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a cewar wani jami’i a jiya Lahadi.

Wasu yan bindiga daga tsohuwar kungiyar yan tawayen hadin guiwa ta Seleka ne suka kaiwa mutanen kauyen Ndomete mai tazarar kilomita 350 daga garin Kaga-Bandoro farmaki, a cewar wani kakakin fadar shugaban kasa Albert Mokpeme.

A cikin watan Maris shekarar 2013 ne Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ta abka cikin rigingimu bayanda dakarun Seleka, wadanda galibinsu Musulmi ne, suka kwace iko wanda hakan ya janyo mayar da martini daga kungiyoyin mayaka na Krista masu kin jinin yan jinsin Balaka.

Kashi biyar na daukacin dukkan mutanen kasar sun gudu daga gidajensu sakamakon tashin hankalin kuma har yanzu kasar ta rabu gida biyu bisa bambancin addini kuma jagabannin mayakan ne ke iko a sassan kasar dab an-daban.

Sama da Mutane dubu dari hudu ne suka rasa matsuganansu a cikin kasar sa’annan karin wasu mutane kamar dubu dari biyar kuma suka nemi mafaka a makwaptan kasashe kamar su Chadi da Kamaru da kuma Junhuriyar Demokradiyyar Congo.

XS
SM
MD
LG