Hare-hare da aka kai a lokaci guda a kasar Kamaru, da ake zargin yan awaren Kamaru da kaiwa, a wasu yankuna biyu na masu amfani da harshen turanci wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama ciki har da sojoji da yan awaren.
Gwamnatin Kamaru tace an kashe mata sojoji da yan awaren da dama. An kona kauyuka da masu yawa haka kuma dubban mutane sun arce yayin da mayakan awaren suka kai hari a kan sansanonin sojoji, su kuma sojojin gwamnatin sun mayar da martani a kan kauyukan da ake zaton suna baiwa yan awaren mafaka. Wakilin Muryar Amurka Moki Edwin Kindzeka ya ziyarci garin Kumbo, inda aka bada rahoton aukuwar hargitsi na baya bayan nan.
Wasu mutanen kauye su talatin yawancin su yara ne, sun nemi mafaka a wani ginin majami’ar Roman Katolika a kauyen Tadu dake kusa da garin Kumbo a yankin arewa maso yammacin kasar na masu amfani da harshen turanci.
Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace ya zuwa watan Janairu, dubban yan Kamaru dake yankin turanin kasar sun ketara zuwa cikin Najeriya kuma an ce taimakon da suke bukata na kara yawa.
Facebook Forum