Shugaban kasar Sudan Salva Kiir ya umarci cibiyar bada tallafi da sake tsugunar da al'umma ta kasar -RCC, ta soke kudin rajista da kungiyoyin sa kai na cikin gida da kuma kasashen ketare dake aiki a Sudan ta Kudu suke biya.
Deng Tong Kenjok, na hukumar ne ya bada umarnin ranar alhamis ga kungiyoyin sa kai a Sudan ta Kudu.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley ta fiyar ta sanarwa jiya Jumma'a tana kira ga gwamnatin Kiir ta samar da kyakkyawan yanayi ga ma'aikatan jinkai dake aiki a Sudan ta Kudu.
Haley tace gwamnati tana bukatar cibiyoyin agaji a Sudan ta kudu su biya tsakanin dala dubu biyu da dubu hudu kan kowanne ma'aikacin kasashen ketare.
Cibiyoyi masu zaman kansu da kuma cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya suna taimakawa wajen gudanar da ayyukan ceton rayukan mutane miliyan uku kowanne wata a Sudan ta Kudu tunda rikici ya barke a shekara ta dubu biyu da goma sha uku.
Facebook Forum