Takaddamar da aka dade ana yi kan sahihancin ‘ya’yan jagoran ‘yan adawar Janhuriyar Nijar Hamma Ahmadu ta dau wani sabon salo. Wannan kuwa ya biyo bayan bullar wata wasikar da aka ce ta fito ne daga Ma’aikatar Shari’ar Tarayyar Najeriya zuwa Ofishin Jakadancin Najeriya a Janhuriyar Nijar dauke da bukatar a gwada kwayar halitta (ko “DNA”) ta matar Hamma Ahmadu mai suna Hadiza Hamma Ahmadu don a tantance sahihancin kasancewar wata yarinya mai suna Fadima Lilian Ahmadu da wani yaro mai suna Ahmadu Guellan ‘ya’yan matar Hamma Ahmadu mai suna Hadiza Hama Ahmadu ne ko a’a.
To saidai lauyan da ke kare matar Hamma Ahmadu din wato Ali Kadiri na ganin wannan ba wani abu ba ne illa wata makarkashiyar sisaya saboda abin mamaki ne a ce gwamnatin Najeriya ta tsoma kanta cikin rigimar siyasar Janhruiyra Nijar. Malam Kadiri ya ce wani abin da ya kara kawo shakku kan sahihancin wasikar shi ne yadda aka yi wasikar da ya kamata a ce ta sirri ce ta wanzu tsakanin jama’a. Don haka, in ji Kadiri, sun a ganin wannan wasikar wasu mahassada ne kawai su ka kirkiro ta su ka wanzar da ita tsakanin ‘yan Nijar don kawai su tozarta iyalan Hamma Ahmadu.
Wakilinmu a Yamai Sule Mummuni Barma ya yi yinkurin jin matsayin hukumomi a Janhuriyra Nijar game da wasikar to amma babu wanda ya yadda ya masa bayani a gwamnatance. To sai dai wani babban kusa a jam’iyyar PNDS mai mulki ya ce shi ya yi imanin cewa wannan wasikar daga hukumomin Najeriya ta fito saboda a baya jami’an gwamnatin Najeriya sun zo kan wannan batun. Ya ce yanzu haka yaran na hannun hukumomin Najeriya.
Ga dai wakilinmu a Yamai Sule Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum