Akwai ‘yan sanda guda takwas a cikin wadanda suka mutun, wadanda suka yi kokarin tare maharin a shingen farko na jami’an tsaro inda ya tada bam din jikinsa, a cewar mataimakin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan Nasaratullah Rahimi.
Rahotanni sun ce zaben ‘yan majalisar dokoki na jiya Asabar a Afghanistan ya huskancin hare hare a fadin kasar, yayin da kuma rahotannin suka ce an samu dogayen layin miliyoyin mutane da suka kada kuru’unsu.
Kungiyar Taliban ta yita bada kashedin kai hare hare a kan runfunan zabe da duk wasu harkokin zabe a kasar. Sai dai wannan barazana bai hana dimbin mutane fitowa su kada kuru’unsa ba.
Facebook Forum