Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Neman Wani Gungun Birrai Ruwa a Jallo


Wasu birrai a wajen wasan yara na Guindy a Chennai
Wasu birrai a wajen wasan yara na Guindy a Chennai

Yanzu haka ‘yan uwan marigayin, sun shigar da kara a caji ofis din ‘yan sanda inda suka nemi da bi masu Kadin danuwansu.

Wani gungun birrai ya jefe wani mutum mai shekaru 72 har lahira ta hanyar jifansa da duwatsu a kauyen Tikri a Baghpat Uttar Pradesh na India.

A cewar Jaridar The Indian Times, Daramphal Singh, ya je cikin daji ne domin debo itace ranar a Alhamis sai gungun birran ya far masa ta hanyar jifa da duwatsun blo da suka debo daga wani rushasshen gida da ke cikin dajin.

Bayanai sun yi nuni da cewa daga kan bishiya birran suka rika jefowa Singh duwatsu har suka fi karfinsa.

Dattijon ya samu raunuka a kansa da kirjinsa sanadiyar jifan, ya kuma cika ne bayan da aka kai shi asibiti.

Yanzu haka ‘yan uwan marigayin, sun shigar da kara a caji ofis din ‘yan sanda inda suka nemi da bi masu kadin danuwansu.

Ammam kamar yadda jaridar ta The Indian Times ta ruwaito, ‘yan sanda sun saka lamarin a rukunin “hadari”.

Sai dai ‘yan uwan mamacin sun daukaka kara zuwa hukumomi na gaba domin ba su gamsu da mataki na ‘yan sanda ba.

Kuma tuni har an bai wa ‘yan sanda umurnin su nemo birran.

Rahotanni na nuni da cewa a ‘yan kwanakin nan, munanan hare-haren da birrai ke kai wa a kasar ta India na ci gaba da karuwa.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG