Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Na Jan Kunnen Amurka Kan Yarjejeniyar Makamai


Shugaban Amurka Trump da takwaran aikinsa Putin
Shugaban Amurka Trump da takwaran aikinsa Putin

Rasha ta bayyana cewa ba ta karya ka'idodin yarjejeniyar kayyade harba makami mai linzami ba da suka yi da Amurka lokacin yakin cacar-baka, yarjejeniyar da Amurkan ke shirin ficewa daga ita.

A yau Litinin Gwamnatin Rasha ta bayyana damuwarta game da kudurin Shugaban Amurka Donal Trump, na ficewa daga wata muhimmiyar yarjejeniyar makamai da aka kulla a zamanin yakin cacar-baka wato "Cold War"a turance.

Ta kara da cewa wannan matakin da Amurkan ke so ta dauka ka iya jefa duniya cikin yanayi mai hadari.

Dmitry Peskov, mai magana da yawun Fadar Shugaban Rasha ya fadawa manema labarai cewa, Rasha ba ta karya ka’idojin yarjejeniyar ba, yana mai cewa idan Amurkan ta ce za ta soma kera wasu sababbin makamai masu linzami, ya zama wajibi Rasha ita ma ta shiga kera nata makaman sababbi.

Peskov ya ce jami’an kasarsa suna so su samu karin bayanai akan shirye-shiryen da Amurka ta ke yi game da yarjejeniyar kayyade makamai masu karamin karfi da ke tafiyar karamin zango, a lokacin tattaunawar da za su yi cikin wannan makon da mai bai wa shugaban Amurka shawara akan harkokin tsaro John Bolton.

A yau Litinin Bolton zai gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov da kuma shugaba Vladimir Putin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG