Lamarin rashin tsaro a Arewacin Najeriya tura na dada kaiwa bango domin batun kare jama'ar yankunan da ke fama da matsalolin na kan hanyar zamowa gaskiya.
Kasa da mako daya da hallaka mutane 23 a jihar Sokoto dake Arewa maso Yammacin kasar, an sake kai wasu hare hare akan jama'ar gabashin jihar, wanda ya hada da kisa tare da satar jama'a.
Wata mata Suwaiba Lawal tana cikin wadanda harin da aka kai cikin daren alhamis ya rutsa da su, ta kuma yi bayannin yadda ta ji harbe-harben da ya yi sanadin mutuwar yarinya da take rike da ita.
Bayanai sun nuna cewa an sace jama'ar da ba'a san adadin su ba a wannan harin acewar wani mazaunin garin.
Lokacin da muka tuntubi wani mazaunin garin Abdullahi Haruna Gobir ana gudanar da jana'izar dan sa da aka kashe, amma wani mazaunin garin ya ce yara ne kanana wadanda suka kai harin suna ta harbin mutane.
Wadannan abubuwan da ke faruwa a Arewacin Najeriya suna saka talaka cikin halin kunci bayan matsin rayuwa da yanayin arzikin kasar ya jefa jama'a ciki a cewar Shugaban kungiyar Muryar talaka Zaidu Bala kofar Sabuwa.
Ya ce basu san abinda gwamnati ke ciki ba ahalin da ake ta kai masu hare hare da kisan gilla. Matasan Najeriya ma sun nuna fushin su har suna nuna yatsa akan gwamnatin kasar.
Duk wannan halin da jama'a suka samu kansu ciki, babban abinda wasu mahukunta ke yi shine jaje tare da yin alkawuran da babu tabbas ga cika su.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir: