Kusan kowace rana ba za a rasa samun rahoton kisa ko satar jama'a don neman kudin fansa ba.
Lamarin rashin tsaro a iya cewa ya kai makura a Najeriya musamman a yankin arewacin kasar, inda ‘yan fashin daji ke baje hajar su yadda suka ga dama.
A jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar ‘yan fashin dajin na ci gaba da addabar jama'a musamman na yankin gabashin jihar, kamar abin da ya faru tsakanin kananan hukumomin Sabon Birni zuwa Isa, inda mahara suka tare wasu matafiya suka cinna musu wuta cikin mota.
Bayanai daga wata majiya da ke kusa da asibitin Isa, inda aka kai wadanda hare haren sun nuna cewa lamarin akwai ban tausayi.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da aukuwar lamarin sai dai a cewar kakakinta a Sakkwato, ASP Sanusi Abubakar ana kan gudanar da bincike.
Tashin hankali dai kusan ace ya zamo abokin zama ga jama'ar gabashin Sakkwato sanadiyyar ayyukan ‘yan fashin daji.
A wannan makon kadai mahara sun afka wa al'ummomi da dama a cewar Tsohon shugaban karamar hukumar Sabon Birni, Idris Muhammad Gobir.
‘Yan Najeriya dai na ci gaba da kiraye kiraye ga mahukunta akan su kara azama ga fafatukar samar da tsaron da suke yi tun kafin ‘yan bindiga su kare jama'ar yankunan da suke addaba.
Saurari cikakken rahoton Muhammadu Nasir: