Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 72 a Tarzomar Afirka ta Kudu


An kashe mutane saba'in da biyu a tarzoma da kuma kwasar ganima a Afirka ta Kudu, in ji ‘yan sanda, yayin da ake zanga-zangar nuna adawa da tsare tsohon shugaban kasar Jacob Zuma.

Rikici ya barke a makon da ya gabata lokacin da Zuma ya fara zaman kurkuku na tsawon watanni 15 saboda raina kotu.

A cikin rikice-rikicen kasar mafi muni a cikin shekarun da suka wuce, masu satar dukiyoyi sun lalata manyan wuraren kasuwanci, da sauran wuraren sayar da kayayyakin kasuwanci a lardin Gauteng, tare da babban birnin Johannesburg, da lardin mahaifar Zuma, KwaZulu-Natal da ma Soweto. Jami'an tsaro sun gaza hana tarzoman da sace-sace da barnar dukiyoyin jama’a.

Masu zanga-zangar sun kuma hau kan tituna don yin tir da matsalar tattalin arziki wanda ya karu sandiyar annobar Coronavirus a shekarar da ta gabata.

Karin mutanen da suka mutu ya zo ne yayin da Afirka ta Kudu ta sanar da cewa za ta tura dubunnan sojoji don karfafa jami’an ‘yan sanda cikin jihohi biyu.

'Yan sanda sun fada jiya Talata cewa yawancin mace-macen sun samo asali ne daga turmutsitsin da ya faru yayin sace-sace da barnar dukiyoyi. An kame sama da mutane 1,000 tunda aka fara zanga-zangar a makon da ya gabata.

A cikin jawabin da ya gabatar wa ‘yan kasar a daren Litinin, Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi tir da tashin hankali da kuma wawure dukiyar kasa, yana mai kira da a kwantar da hankali.

Gidauniyar Zuma ta ce ba za a sami zaman lafiya ba muddin tsohon dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata ya kasance a bayan gidan yari.

Gidauniyar ta rubuta a shafin ta na Twitter cewa "Zaman lafiya da kwanciyar hankali a Afirka ta Kudu suna da nasaba da sakin Shugaba Zuma kai tsaye ba tare da bata lokaci ba."

XS
SM
MD
LG