Wata kotu a Afirka ta Kudu, ta ba da sammacin kama tsohon shugaban kasar Jacob Zuma, saboda ya ki bayyana a gaban kotu a yau Talata a zaman shari’ar da ake tuhumarsa da wasu laifuka.
Ana zargin Zuma ne da laifin karbar cin hanci daga wani kamfanin Faransa mai kera makamai da ake kira Thales, wanda ya rattaba hannu kan wani kwantiragin dala biliyan biyu da kasar.
Lamarin ya faru ne a shekarar 1999, a lokacin Zuma na matsayin mataimakin shugaban kasa.
A daukacin karar, ana tuhumar Zuma da laifuka 16, wadanda suka hada da damfara da zamba cikin aminci.
Su dai lauyoyin Zuma, sun gabatar da wata wasika da wani likitan sojoji ya sa hannu, wacce ta nuna cewa tsohon shugaban ba shi da lafiya, ya kuma fita kasar waje ganin likitoci - wasikar da alkalin ya nuna shakku akai.
Sai dai alkalin, ya jingine sammacin kama Zuma zuwa ranar 9 ga watan Mayu, lokacin da za a sake zaman sauraren karar.
Facebook Forum