Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zuma Ya Ba Da Bahasi a Gaban Kwamitin Da Ke Bincikensa

Shugaban alkalan da ke binciken Raymond Zondo, ya ce, ba hurumin kwamitin ba ne ya ayyana cewa wani na da laifi a wannan zama, sai dai aikin kwamitin ne ya gudanar da binciki kan wasu zarge-zarge da ake yi.

Tshohon shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya ba da bahasi a gaban wani kwamitin bincike kan zargin cin hanci da ake masa a zamanin mulkinsa na farko.

A yau Litinin, Zuma ya fadawa kwamitin binciken cewa, akwai bita da kulli da ake masa sannan akwai wata makarkashiyar da ake kullawa ta kokarin ganin an kawar da shi daga fagen siyasar kasar.

Tsohon shugaban kasar ta Afrika ta Kudun ya kuma ce an kwashe sama da shekaru 20 ana kokarin ganin an bata mai suna.

Shugaban alkalan da ke binciken Raymond Zondo, ya ce, ba hurumin kwamitin ba ne ya ayyana cewa wani na da laifi a wannan zama, sai dai aikin kwamitin ne ya gudanar da binciki kan wasu zarge-zarge da ake yi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG