WASHINGTON DC - Babban Sufeton 'Yan Sandan ya bayyana hakan ne yayin taron Hukumar Gudanarwar Rundunar a Alhamis din nan.
Ya kara da cewar, wadanda aka kama din na taimakawa rundunar da bayanan da zasu kai ga kama mutanen dake da hannu a kisan.
A ranar 23 ga watan Febrairun daya gabata ne, aka hallaka jami'an 'yan sanda 6 a dajin Ohoro, dake Karamar Hukumar Ughelli ta Arewa a jihar Delta.
A wani labarin kuma, wadansu mutanen 6 da ake zargi da hannu a kisan sun tsere.
Kisan na zuwa ne a daidai lokacin da aka hallaka hafsoshin soja 17 a jihar ta Delta mai arzikin man fetur.
An hallaka sojojin ne a yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a kauyen okuama dake Karamar Hukumar Ughelli ta Kudu a wani al'amari daya janyo allawadai a fadin Najeriya.
A yayin jana'izar sojojin data gudana a makon daya gabata, hukumomin sojin Najeriya sun sha alwashin farauto wadanda suka kitsa harin, tare da jaddada cewar hakan ba zai hana su cimma burinsu na fatattakar batagari daga fadin Najeriya ba.
Haka shima, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya mika lambobin girmamawar kasa ga sojojin da hallaka tare da daukar nauyin karatun 'ya'yansu.
Dandalin Mu Tattauna