Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mutane 8 Da Ake Zargi Da Alaka Da Kungiyar IS A Amurka


An kama wasu mutane takwas daga kasar Tajikistan da ake zargin suna da alaka da kungiyar IS a Amurka a cikin 'yan kwanakin nan, a cewar wasu da ke da masaniya kan lamarin.

An kama mutanen ne a biranen New York da Philadelphia da Los Angeles.

Mutanen sun shiga Amurka ne ta kan iyakar kudancin kasar, ana tsare da su ne kan keta dokar shige da fice, in ji mutanen, wadanda suka ce ba su da izinin tattaunawa kan binciken da ake yi, kamar yadda su ka shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press.

Immigration Police
Immigration Police

Ba a fayyace yanayin alakarsu da kungiyar ba, amma hukumar hadin gwiwa ta FBI, ta yi ta bin diddigin mutanen.

Yanzu haka su na hannun Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka da Hukumar Kwastam, har zuwa lokacin da za a yi shari’ar fitar da su daga kasar.

Hukumar FBI da Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida sun fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da kamun da aka yi wa "wadanda ba 'yan kasar da dama" da suka shafi shige da fice ba amma ba su yi cikakken bayani ba.

Daraktan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Christopher Wray, ya ce Amurka na fuskantar karin barazana daga masu tsatsauran ra'ayi na gida da kuma kungiyoyin 'yan ta'adda na kasashen waje, musamman bayan harin da Hamas ta kai kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.

Hukumomin sun ce "FBI da Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida za su ci gaba da aiki ba dare ba rana, tare da abokan aikinmu don ganowa, bincike, da kuma dakile barazanar da za a iya yi wa kasa."

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG