Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dan Jaridan Najeriya a Nijar


'Yan jarida na tserewa wani yanki da ake rikici a Libya
'Yan jarida na tserewa wani yanki da ake rikici a Libya

Rahotanni daga birnin Agadez da ke kasar Jamhuriyar Nijar na nuna cewa an kama wani dan jaridar Najeriya da ye je yin bincike kan yadda ‘yan nahiyar Afrika ke bi ta kasar domin kaiwa ga kasashen turai.

Birnin Agadez ya kasance mashigi ne ga masu zuwa arewacin Afrika domin isa kasashe irinsu Libya inda dubban ‘yan Afrika ke kwarara domin kai wa ga turai ta kan tekun Meditareniya.

Shi dai Dan jaridar mai suna Lawan Adamu, ya na aiki ne da kamfanin Media Trust da ke buga jaridar Daily Trust a matsayin mataimakin Edita.

Rahotanni sun ce an cafke shi ne a wajen garin na Agadez duk da cewa ya nemi iznin shiga kasar tare da samun takardu daga ofishin jakadancin Nijar din da ke birnin Kano a Najeriya.

‘Yan Afrika da dama kan mutu yayin kokarin ketara hamada domin kaiwa ga kasar Libya, baya ga hakan, daruruwa sun mutu akan tekun bayan da kwalakwalensu ya kife.

Yanzu haka wannan matsalar kwararar ‘yan gudun hijra daga yankunan Asiya da Afrika sun haifar da matsalar bakin haure a wasu kasashen turai yayin da suke gujewa abinda wasu ke dangantawa da talauci da yake-yake.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin Nijar ba su ce uffan game da cafke dan jaridar ba.

XS
SM
MD
LG