A cikin dakin kotun da ya cika makil da jama’a a Vancouver a Canada, wani lauyan gwamnatin kasar ya musunta baiwa Meng Wanzhou, babbar jami’an kudi na katafaren kamfanin fasaha na kasar China Huawei beli a jiya Juma’a, yayin da ake nazarin yiwuwar mikata ga Amurka kuma yace tana da hadari ga sufurin jirgin sama
Lauyan mai shigar da karar yace Amurka tana neman Meng bisa zarginta da yaudarar ma’aikatun kudi a kan huldan Huawei da wani kamfanin fasaha na SkyCom dake Hong Kong da ake zarginsa da sayarwa Iran wasu na’urar fasaha da Amurka ta kera, wanda hakan ya sabawa takunkumin cinikayya da Amurka ta kakabawa Iran.
Kama Meng a birnin Vancouver da Amurka ta buakaci hakan daga Canada, ya zo da mamaki ga kasuwar hada-hadar kudi, bayan Shugaba Donald Trump da takwarar aikinsa na China Xi Jinping sun amince a kan wata yarjejeniyar ciniki a karshen mako a Argentina.
Facebook Forum