Wani jirgin ruwa mai dauke da mutane 20, wanda ake tunanin Musulman Rohingya ne, ya isa tsuburin Sumatra da ke kasar Indonisiya.
Wannan kaurar da ‘yan Rohingyan suka yi, ita ce ta baya-bayan nan da ta auku a ci gaba da zargin cin zarafinsu da ake yi a Myanmar.
A kwanan nan, mahukuntan Myanmar sun hana wasu jiragen ruwa cike da ‘yan Rohingya zuwa kasar Malaysia.
‘Yan gudun hijirar suna tserewa ne daga wani sansanin da aka ajiye su wanda ke dauke da sama da mutane 700,000 a Bangladesh. Inda suke neman mafaka bayan hare-haren da aka kai musu a Myanmar a shekarar da ta gabata a jihar Rakhine.
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi sojojin Myanmar da aikata laifin kisan kare dangi, zargin da suka musanta.
Facebook Forum