Jami’ai a kasar Masar sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a shingen binciken motoci a Arewacin Sinai, ya kashe sojoji 10.
Har yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin kusa da garin Rafah a yau Juma’a.
Masar dai na fama da hare-haren ta’addanci tun shekarar 2013, lokacin da sojoji suka hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi, bayan wata gagarumar zanga-zanga.
A daya bangaren kuma, daruruwan mayakan ISIL na ta kokarin ganin sun sami ikon wani yankin birnin Mosul a Iraqi, amma a jiya Alhamis kwamandojin Iraqi da jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce dubban fararen hula sun makale a yankin, kuma suna cikin hatsari kasancewar fadan da ake yi.
Mayakan ISIL dai sun takurawa iyalai da ‘yan uwansu wajen shiga yakin da ake yi a Mosul, wanda yanzu haka ya zo karshe, sojojin Iraqi sunc e mayakan sun yi wa fararen hular barazanar kashe duk wani da ya yi kokarin guduwa daga yankin.
Facebook Forum