Jami’ai sun ce an kai wa wasu malamai hudu na kwalejin Cornell ta Iowa da ke koyarwa a jami’ar China hari a wani wurin shakatawa na jama’a, inda aka rawaito an kai harin da wuka.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Sin, a yau Talata, ya ce, an kai wadanda suka jikkata asibiti, kuma babu wanda ke cikin mawuyacin hali.
Ya ce ‘yan sanda sun yi imanin cewa harin da aka kai a ranar Litinin wani lamari ne na daban.
Yayin tabattar da lamarin, Shugaban kwalejin Cornell Jonathan Brand a wata sanarwa da ya fitar ya ce, an kai wa malaman hari ne a wurin shakatawa lokacin suna tare da wani malami daga jami’ar Beihua, inda Amurkawan ke koyarwa.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce tana sane da rahotannin harin da aka kai da wuka kuma tana sa ido kan lamarin.
Dandalin Mu Tattauna